Galatians 4

1Abin da nake faɗi shi ne, muddin magāji, yaro ne, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome. 2Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa. 3Haka yake, saʼad da muke yara, muna cikin bauta a ƙarƙashin ƙaʼidodin duniya. 4Amma da lokaci ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffen mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka, 5domin yǎ fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, don mu sami cikakken matsayin ʼyaʼya. 6Domin ku ʼyaʼya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake yin kira, “Abba,
Aramayik na Mahaifi
Uba.”
7Saboda haka kai ba bawa ba ne, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.

Damuwar Bulus domin Galatiyawa

8Dā saʼad da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda bisa ga ainihi ba alloli ba ne. 9Amma yanzu da kuka san Allah-ko kuma a ce Allah ya san ku-ta yaya kuke sāke komawa ga ƙaʼidodi marasa ƙarfi abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu? 10Kuna kiyaye ranaku da watanni da lokatai da shekaru na musamman! 11Ina tsoro, cewa wataƙila na yi wahala a kanku a banza!

12Ina roƙonku ʼyanʼuwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba. 13Kamar yadda kun sani, saboda rashin lafiya ne na yi muku waʼazin bishara da farko. 14Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce malaʼikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa. 15Me ya faru da dukan farin cikinku? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni. 16Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan? 17Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar nufi ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yǎ koma musu. 18Yana da kyau ku yi ƙwazo, in dai manufar tana da kyau, ku kuma kasance haka kullum ba sai ina tare da ku ba. 19Ya ku ʼyaʼyana ƙaunatattu, waɗanda nake sāke shan zafin naƙuda saboda ku, sai ran da Kiristi ya kahu a cikinku, 20da ma a ce ina tare da ku yanzu in kuma canja muryata, domin na damu ƙwarai saboda ku!

Saratu da Hagar

21Ku gaya mini, ku da kuke so ku zauna a ƙarƙashin Doka, ba ku san abin da Doka ta ce ba? 22Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da ʼyaʼya biyu maza, ɗaya ta wurin baranyar mace, ɗaya kuma ta wurin ʼyantacciyar mace. 23Ɗansa na wajen baranyar bisa ga ƙaʼidar jiki ne; amma ɗansa na wajen ʼyantacciyar a sakamakon alkawarin ne. 24Waɗannan alʼamura za a iya ɗaukansu a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawarai biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ʼyaʼyan da za su zama bayi: Hagar ke nan. 25Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima, domin ita baiwa ce tare da ʼyaʼyanta. 26Amma Urushalimar da take sama ʼyantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu. 27Domin a rubuce yake cewa:

“Ki yi farin ciki, Ya ke bakararriya,
wadda ba ta haihuwa
ki ɓarke da murna, ki kuma ta da murya,
ke da ba kya naƙuda;
domin da yawa ne ʼyaʼyan macen da aka yashe,
fiye da na mai miji.”
Ish 54.1

28To, ku ʼyanʼuwa, kamar Ishaku, ku ʼyaʼyan alkawari ne. 29A lokacin nan, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙaʼidar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu. 30Amma mene ne Nassi ya ce? “Kori baranyar da ɗanta don ɗan baranyar ba zai taɓa gādo tare da ɗa na ʼyantacciyar ba.”
Far 21.10
31Saboda haka, ʼyanʼuwa, mu ba ʼyaʼyan baranyar ba ne, amma na ʼyantacciyar.

Copyright information for HauSRK